Ministan harkokin wajen Isaraila ya fara ziyarar neman goyon bayan Turai game da Hamas | Labarai | DW | 01.03.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ministan harkokin wajen Isaraila ya fara ziyarar neman goyon bayan Turai game da Hamas

Ministan harkokin wajen Israila,Tzipi Livni, a yau zai fara kawo ziyara nan turai, a wani kokarin tabbatar da hadin kai dangane da batun kungiyar Hamas.

Lashe zaben da kungiyar tayi dai,ya sanya Israila ta dakatar da dukkan taimakon kudi da take baiwa hukumar Palasdinawa.

Kasashen turai da dama da kuma Amurka,suna goyon bayan Israila game da bukataunta da kungiyar Hamas,na cewa dole ta amince da kasancewar Israila kasa.

Kasar ta Israila dai a yanzu,ta baiyana damuwarta dangane da gaiyata da Rasha tayiwa manyan jamian Hamas zuwa Rasha nan gaba cikin wannan mako.

Rasha a nata bangare tace zata matsawa Hamas ta amince da bukatun Israila.

Ministan na Israila zai kai ziyara irin wannan zuwa kasashen Faransa,Burtaniya da Austria.