Mexiko da Turai za su sabunta yarjejeniyar kasuwanci
June 12, 2015Talla
Kasar Mexiko da kungiyar kasashen Tarayyar Turai sun amince da kaddamar da tataunawa kan kulla sabuwar yarjejeniyar cinikayya tsakanin bangarorin biyu.
Shugaba Enrique Pena Nieto na kasar ta Mexiko ya bayyana haka wa manema labarai a birnin Brussels na kasar Beljiyam, inda ya nunar da mahimmancin haka saboda yadda Amirka da Kanada suka zama manyan masu hulda da kasar. Sabon matakin zai taimaka wa Mexiko ta shiga jerin kasashen da suka sabunta yarjejeniya ta zamani da kasashen Tarayyar Turai.