Merkel za ta tattauna da SPD da CSU | Labarai | DW | 13.12.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Merkel za ta tattauna da SPD da CSU

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel na shirin ganawa da shugabannin jam'iyyar SPD da CSU domin tattauna batun kula wani sabon kawance don kafa gwamnati.

An shirya za a fara tattauna zagaye na farko tsakanin Angela Merkel da jagoran SPD Martin Schulz da kuma jagoran jam'iyyar CSU Horst Seehofer a wani wurin da ba a bayyana ba. Watannin uku ke nan ya zuwa yanzu bayan kammala zaben 'yan majalisun dokoki a Jamus, har yanzu ba a kafa gwamnati ba saboda rashin samun sulhu tsakanin jam'iyyun siyasar kasar.