1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MDD ta je tashar makamashin Zaporizhzhya

Abdul-raheem Hassan
August 29, 2022

Kwararru daga hukumar kula da makamashin nukiliya ta Majalisar Dinkin Duniya, sun ziyarci tashar Zaporizhzhya a Ukraine, yayin da yakin Rasha da Ukraine ke cigaba da barazana ga babbar cibiyar nukiliyar Turai mafi girma.

https://p.dw.com/p/4GBJc
Hukumar kula da makamashin nukiliya ta Majalisar Dinkin Duniya
Hoto: Alex Halada/AFP/Getty Images

Manyan kasashen duniya sun yi gargadi game da yuwuwar bala'in nukiliya a tashar Zaporizhzhya, inda ake yawan kai hare-hare. Sai dai Kiev da Moscow sun sha musanta kai hari a kan tashar. Sai dai Shugaban Faransa Emmannuel Macron ya ce wajibi a kare tashar. "Wannan yakin ba zai iya gurgunta tsaron nukiliya ba, don haka wannan manufa na na ziyarar kwararru na da mahimmanci, dole a kare wannan tashar makamashin nukiliya tare da tabbatar da kariya ga duk yankin. Ikon Ukrain na mallakar wannan tasha ba za a kalubalance ci ba. Ikon nukiliya bai kamata ya zama wani abu na yaki ba, kuma yana da mahimmanci a kare hakkin Ukrainian a kan wannan tashar makamashi."