1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

MDD: Al'ummar yammaci da tsakiyar Afirka na fama da yunwa

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
April 13, 2024

Majalisar ta ce kasashen da bala'in yunwar ya fi ta'azzara sun hada da Najeriya da Ghana da Salo da kuma Mali

https://p.dw.com/p/4eiSE
Hoto: Sascha Steinach/dpa/picture-alliance

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa mutane miliyan 55 ne ke fuskantar barazanar yunwa a yammaci da kuma tsakiyar nahiyar Afirka, sakamakon tashin farashin kayan masarufi da ya jefa al'umma cikin halin kaka naka yi wajen samun abin da za su ci.

Karin bayani:Najeriya: Kokarin magance matsalar karancin abinci

Wata sanarwar hadin gwiwa da hukumomin majalisar suka fitar, da suka hada mai kula da abinci WFP da ta UNICEF mai kula da kananan yara, da kuma ta harkokin noma, sun ce kasashen da bala'in yunwar ya fi ta'azzara sun hada da Najeriya da Ghana da Salo da kuma Mali.

Karin bayani:Najeriya: Al'umma cikin kangin talauci

Sanarwar ta kara da cewa dogaro da kasashen suka yi wajen shigo da kayan abinci daga ketare, na daga cikin dalilan kara kamarin hauhawar farashin kayan masarufin da dangoginsu, musamman ma a Najeriya da Ghana da kuma Salo.

Babban jami'in hukumar kula da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya mai kula da shiyyar Afirka ta yamma Robert Guei, ya ce tilas ne mahukuntan kasashen su bijiro da tsarin habaka noma da sauran hanyoyin samar da abinci a cikin gida, domin dakile wannan masifa da ke addabar al'ummarsu.