1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Boko Haram ta hallaka sojojin Najeriya

Binta Aliyu Zurmi
September 16, 2021

Sojojin Najeriya da wasu 'yan Civilian JTF sun rasa rayukansu a wani hari da mayakan ISWAP.

https://p.dw.com/p/40QMz
Nigeria - Boko Haram Konflikt
Hoto: picture alliance/dpa

Rahotanni da shiyyar Arewa maso Gabashin Najeriya na nuna da cewa mayakan Kungiyar ISWAP sun hallaka sojojin Najeriya 16 da wasu matasan Civilain JTF guda biyu gami da raunata wasu a wani harin kwanton bauna da mayakan su ka kai wa tawagar Sojojin a kan hanayar Munguno zuwa Maiduguri da yammacin jiya. 

Cikin wadanda su ka jikkata har da kwamandan sojojin da ke jan tawagar inda kuma ake fargabar mayakan sun tafi da Sojojin biyu kamar yadda waasu majiyoyin da ke bin hanyar su ka tabbata.

Wannan harin dai ya yi muni saboda salon da mayakan su ka dauka na yin a cewar masu bin hanyar da su ka shaida abun da ya faru su ka bayyana.


Ya zuwa wannan lokaci dai humumomin Sojojin ba su ce komai kan wannan harin ba.