1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojojin Najeriya 7 sun mutu a harin ta'addanci

Ramatu Garba Baba
October 11, 2018

Sojojin sun halaka ne a yayin da suka yi yunkurin dakile harin da mayakan suka kan sansaninsu da ke a kauyen Metele na jahar Borno a shiyyar Arewa maso Gabashin kasar da ya sha fama da ayyukan ta'addanci.

https://p.dw.com/p/36Khu
Nigeria Boko Harem Angriff in Damaturu
Hoto: picture-alliance/AP

Rundunar tsaron kasar ce ta wallafa labarin a shafinta na Twitter, ta kuma ce akwai wasu akalla goma sha shida da suka sami rauni daga artabun. Mayakan sun far ma sansanin da ke kauyen Metele na jahar Borno kuma an kwashi akalla sa'oi bakwai ana gwabza fada a tsakanin bangarorin biyu inji sanarwar.

Wani jami'in soji da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce sojojin sun nuna kwazo a yayin da suke kokarin dakile harin na bazata sai dai mayakan sun ci karfinsu saboda yawansu. A ranar Litinin da ta gabata aka kai harin, an gano mayakan na Boko Haram sun sace wasu makamai kafin su bar sansanin baya ga wadanda suka lalata.