Matsalolin canjin yanayi da ta′addanci a yankin tafkin Chadi | Siyasa | DW | 24.10.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Matsalolin canjin yanayi da ta'addanci a yankin tafkin Chadi

Kokarin samun mafita daga matsalolin da rikicin Boko Haram da na sauyin yanayi suka jefa yankin tafkin Chadi a ciki.

A Nijar an gudanar da wani taron tattaunawa na wani bincike da wata cibiya ta kasar Jamus ta gudanar kan yankin tafkin Chadi game da matsaloli na Boko Haram da kuma na sauyin yanayi da ke addabar yankin domin samun mafita.

Wannan bincike dai ya samu tallafi ne daga kasashen Holland da kuma Jamus a kokarinsu na ganin an samo bakin zaren warware matsalar da ke addabar yankin tafkin Chadi mai fama da matsaloli na 'yan tarzoma musamman Boko Haram.

A shekara ta 2018 dai an gudanar da wani babban taro na neman mafita kan yankin na tafkin Chadi a birnin Berlin na kasar Jamus, kuma wannan bincike na daga cikin matakan da aka dauka na bin hanyoyin kawo sauyi da ci-gaba a yankin.

Hermann Nicolai shi ne jakadan kasar Jamus a Nijar ya ce: ''Hadin gwiwar tsarin Majalisar Dinkin Duniya mai kula da ci-gaban kasashe na UNDP da Jamus na kokarin ganin an samu daidaituwar al'amura a yankin na tafkin Chadi, inda barazanar sauyin yanayi da ta 'yan ta'adda ke zama babban cikas ga rayuwar mazaunan yankin.

Sauti da bidiyo akan labarin