Matsalar tsaro na karuwa a Tillaberi da ke Nijar | Siyasa | DW | 05.05.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Matsalar tsaro na karuwa a Tillaberi da ke Nijar

Wasu kungiyoyin mazauna yankin Tillabery da ke Jamhuriyar Nijar, sun fara nuna kosawarsu da yadda matsalar tsaro ke kara kamari, duk da alkawarin da shugaban kasa Mohamed Bazoum ya dauka na shawo kan matsalar.

Nigeria I Präsidenten Mohamed Bazoum

Sabon shugaban kasar Jamhuriyar Nijar Mohamed Bazoum

Sojoji da ma fararen hula da dama ne dai suka halaka, sakamkon wani hari da mayakan 'yan ta'adda suka kai kauyen Ntoussane da ke gundumar Banibangou a cikin jihar Tillaberi da ke Jamhuriyar Nijar. Bayanai daga yankin na Tillaberi na cewa da yammacin Talatar da ta gabata ne, 'yan ta'addan kimanin 200 a kan baburra suka kaddamar da farmaki kan kauyen, inda suka rabu gida biyu kaso daya ya tunkari sojojin da ke jibge a kauyen yayin da kaso na biyu ya shiga kauyen na Ntoussane tare da yin harbin kan mai uwa da wabi.

Karin Bayani: Sabuwar gwamnati ta kama aiki a Nijar

Wani mazaunin kauyen na Ntoussane ya shaidawa DW ta wayar tarho yadda lamarin ya afku cikin halin dimuwa: "Sun zo a kan babbura, wadanda za a iya cewa sun fi 1,000. Wasunsu na dauke da mutane uku wasu kuma biyu, a gaskiya ba zan iya bayyana adadinsu ba. A gabana aka fara dauki ba dadin ina labe a wani wuri. Wasu 'yan ta'addan sun hau kan tudun kauyen, saura kuma suka tsaya kewayen garin wanda daga karshe suka yi masa zobe. Ana cikin haka sojoji suka iso amma a gaskiya ni ban lura da sun iso ba ma saboda rashin yawansu. Daga karshe 'yan ta'addan sun ci karfinsu, inda suka halaka da dama. Wasu sojojin da suka ji rauni sun nemi mafaka a gidajenmu. Amma ni kaina na ga gawarwakin sojoji 14."

Cartoon Niger, Sicherheit/Politik Lage

Baya ga matsalar tsaro, akwai tarin kalubale ga gwamnatin Mohamed Bazoum

Wasu bayanai dai sun nunar da cewa, sojoji 16 ne da fararen hula hudu suka halaka a cikin harin. Sai dai kungiyar da ke fafutukar kare yankin na Tillabery, ta bakin shugabanta Malam Amadou Harouna Maiga ta nuna bacin ranta da kuma mamakin yadda sojoji ke ci gaba da kare kai a maimakon farautar 'yan ta'addar da ke kai hare-haren a maboyunsu da ma kuma yadda matsalar tsaron ta ki yin sauki, duk da alkawarin da shugaban kasa Mohamed Bazoum ya yi na tunkarar matsalar da zarar ya hau mulki.

Karin Bayani: Bazoum zai yi aiki da kasashe makwabta

To amma a kokarin da kasashen Turai ke yi na taimaka wa Nijar, a Talatar da ta gabata Jamus da kungiyar kasashen Turai mai kula da harkokin tsaro a Sahel wato EUCAP da kuma gwamnatin Nijar, sun cimma yarjejeniyar daukar nauyin wata rundunar tsaro ta sintirin kan iyakoki da za a kafa a yankin iyakoki uku na Nijar da Mali da kuma Burkina Faso, inda 'yan ta'adda ke zafafa kai hare-hare a yanzu domin tabbatar da tsaro. Ministan cikin gida na Nijar Alkach Alhada ya bayyana cewa rundunar sintirin na da fa'ida sosai. Har ya zuwa lokacin hada wannan rahoto dai, gwamnati ba ta ce komai ba kan harin, kuma kokarin da muka yi na jin ta bakin duk wani mukaddashin gwamnati a yankin na Tillaberi ya ci tura.

Sauti da bidiyo akan labarin