1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Barazanar tsaro a Nijar bayan zabe

Lateefa Mustapha Ja'afar
January 7, 2021

Wani mummunan hari da 'yan ta'adda su ka kai a Jamhuriyar Nijar, ya halaka mutane da dama. Shin ko me hakan ke nufi ga fannin tsaro a kasar, a daidai lokacin da aka shiga sabuwar shekara ta 2021?

https://p.dw.com/p/3ndoZ
Niger Symbolbild Terror
Hoto: Boureima Hama/AFP

Harin dai na zuwa ne jim kadan bayan kammala zaben shugaban kasa zagaye na farko a Jamhuriyar ta Nijar, da ya bai wa 'yan takara biyu damar sake fafatawa a zagaye na biyu. 

Rahonanni sun nunar da cewa kimanin mutane 100 da suka halaka a cikin wani ta’addanci da aka kai a karshen makon da ya gabata a wasu kauyukan kasar da ke kan iyaka da Mali. 

Za dai a iya cewa, shekara ta 2021 ta zowa Jamhuriyar ta Nijar cikin yanayin kalubale na harin 'yan ta'adda, baya ga annobar cutar sankarau da ake fama da ita a Damagaram a daidai lokacin da ake fama da annobar cutar coronavirus.