1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Farmaki a kan ofisoshin INEC a Najeriya

Muhammad Bello AH/RGB
December 13, 2022

Ana zargin 'yan haramtacciyar kungiyar rajin kafa kasar Biafra ta IPOB da laifin kai hari kan babban ofishin hukumar zabe ta kasa da ke Jihar Imo a kudancin Najeriya.

https://p.dw.com/p/4Kpia
Shugaba Muhammadu BuhariHoto: Siphiwe Sibeko/REUTERS

Ana zargin mayakan Kungiyar IPOB din ne, suka rinka jefa bama-bamai tare da harbe-harben kan mai uwa da wabi a hedikwatar hukumar ta zabe a Jihar ta Imo, ko da yake jami'an tsaro sun yi artabu da su, harin ya yi barna matuka a ofishin na INEC musamman ma ofishin da hukumar ke adana bayanai. Jami'an tsaron sun ce, sun bindige 'yan bindigar uku har lahira.

Wannan harin dai na zuwa ne bayan kwanaki takwas bayan wani hari da 'yan bindigar suka kai kan wani ofishin hukumar da ke karamar hukumar Orlu a a jihar ta Imo, har wa yau, sun kai wani hari na dabam, a baya-bayan nan a kan ofishin na INEC da ke a Jihar Ebonyi a yankin kudancin Najeriyar. 

Karuwar hare-hare kan ofisoshin hukumar zabe
Karuwar hare-hare kan ofisoshin hukumar zabeHoto: Uwais Abubakar Idris/DW

Hukumar ta INEC tuni ta koka kan wasu hare-haren a wasu sassan kasar ,da ma rundunonin tsaro a yankin na Ibo, musamman a yanzu da 'yan sanda ke ci gaba da tabbatar da cewar zabukan na 2023 , za su gudana, ba kuma gudu ba ja da baya cikin kwanciyar hankali.

Nnamdi Kanu
Jagoran Kungiyar IPOB Nnamdi KanuHoto: Katrin Gänsler/DW

Bayan dai hare-hare kan ofisoshin hukumar ta INEC da 'yan bindigar na IPOB ke yi a yankin ,tare da lasar takobin da suka yi na cewar ba za su bari zaben na 2023 ya gudana ba a yankin, hare-haren kan kai ga kan jama'ar yankin da ba su ji ba, ba su gani ba, musamman ma 'yanci rani, inda bayanai suka nunar da daman jama'a sun halaka sakamakon wadannan harehare.

Tuni Hukumar INEC ta koka kan wasu hare-haren a wasu sassan kasar da ma rundunonin tsaro a yankin na Ibo, musamman na 'yan sanda na ci gaba da tabbatar da cewar, zabukan na 2023 za su gudana, ba kuma gudu ba ja da baya , sannan a cikin kwanciyar hankali.