1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalar tsaro a Najeriya

April 30, 2021

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya a 'yan kwanakin nan, na shan matsin lamba daga ciki da wajen jam'iyarsa da ma yan adawa dangane da batun shawo kan kalubalen tsaro da ya dabarbarta lamurra a kasar.

https://p.dw.com/p/3soFD
Muhammadu Buhari
Hoto: picture-alliance/dpa/M. Kappeler

Hare-haren yan bindiga tare da garkuwa da mutane sun ta'azarra a wannan watan na Apirilu a kasar mai mafiya yawan al'umma a nahiyar Afirka. A makon da ya gabata kachal, akalla mutane sama 240 aka salwantar da rayuwarsu wasu gwammai kuma aka yi garkuwa dasu.

Yan adawa da ma daidaikun al'umar kasar sun zargi shugaban da gazawa wajen tabbatar da tsaro a yankunan kasar, inda aka kiyasta cewa kimanin mutane sama da miliyan biyu ne ke gudun hijira a kasashe makwabata bayan hallaka wasu sama dubu talatin da shida.