Matsalar karancin ruwan sha a jihar Katsina | Siyasa | DW | 17.04.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Matsalar karancin ruwan sha a jihar Katsina

Mazauna birnin Katsina sun gudanar da zanga-zangar lumana kan matsalar ruwan sha da ta addabesu tsawon lokaci su na fuskanta, amma har yanzu mahukunta sun kasa magance masu matsalar.

Masu zanga-zangar sun yi jerin gwano suna zagayawa cikin gari dan nuna takaicinsu kan matsalar ruwan sha Comrade Kabir Yandaki na daga cikin shugabannin Kungiyar Muryar Talaka kuma shiya jagoranci Zanga-zangar:

"Zanga-zangar da muka shirya yau mun shiryata ne don yanayin da al'umma suke ciki na fuskantar matsaloli kama daga matsalar ruwan sha da wutar lantarki. Idan muka duba matsalar ruwa abu ne da ya addabi al'umma. Kusan kashi 85zuwa 90 bisa 100 idan ka kalli yanayin da mutane suke ciki hatta kai ga mutane basu iya sayen ruwa da kudin su domin kurar da ake saye ta ruwa ta kai matakin da ana saidata naira 400 ko 500. Wani wurin 600 kai wani gunma har 1000".

 

Su kansu magidanta a birnin na katsina basu da kwanciyar hankali ga neman abincin iyali ga kuma neman ruwa a cewar MUhammad Danjuma Katsina wani magidanci:

"Matsalar ruwa ta samu Katsina wadda kuma ba'a taba ganin ta ba a tarihin jihar wanda ta jayo har rijiyoyi sun kafe. Mutane su na wuri gurin sai da ruwa wasu kuma su na kai tsakar dare kuma ana sayen jarkar ruwa daga naira 80 zuwa 50 zuwa 25 ya danganta da irin nisanka da inda ake sai da ruwan"

Äthiopien Gurage Zone

Rijiyar burtsatsi a kasar Ethiopiya

.

To ko me mahukunta ke yi kan wannan matsala? Babangida Abubakar shi ne shugaban hukumar samar da ruwan sha a jihar

"Fanfunan mu da ke bada ruwa a ajiwa sun lalace saboda haka gwamnati ta riga ta sawo famfo wanda za'a kara dashi domin a cigaba da bada ruwan nan kamar yadda aka saboda haka muna ba mutane hakuri Gwamnati tana kokarin ta akwai shiri da akayi yanzu zamu samo motoci wadan da zasu bi su rika raba ruwa cikin unguwanni domin rage radadin ruwan nan".

Matsalar ruwan sha da fannin ilmi da wutar lantarki na daga cikin abunda mahukunta a Najeriya ke gangamin yakin neman zabe da su. Sai dai har yanzu babu daya da aka magance.

 

Sauti da bidiyo akan labarin