Matsalar cutar Zika a kasar Banizuwela | Labarai | DW | 12.02.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Matsalar cutar Zika a kasar Banizuwela

Akalla mutane uku ne suka rasu sakamakon cutar Zika a kasar Banizuwela a cewar shugaban kasar Nicolas Maduro cikin wani jawabi da ya yi a ranar Alhamis.

Shugaban ya ce "a fadin kasar ta Banizuwela baki daya, akwai a kalla mutane 319 da aka tabbatar sun kamu da wannan cuta kuma daga cikinsu 68 na cikin mawuyacin hali. Shugaban ya kara da cewa mutanan 68 da ke cikin mawuyacin hali an kebesu a wuri na musamman inda ake yi musu magani na musamman.

Maduro ya ce kasar ta na da isasshen maganin da za ta fuskanci masu alamar cutar ta Zika, inda ya isar da godiyarsa ga kasashen irin su Indiya, Chaina, Iran da Brazil da suka taimaka aka samu isasshen maganin tunkarar wannan cuta a kasar ta Banizuwela.