Wata matashiya a jihar Bauchi mai sana'ar gyaran na'urar kwamfuta ta bayyana cewa ta ga muhimmancin rike sana'a a rayuwa, domin da ita ta ke daukar nauyin karatunta inda yanzu har ta samu kammala NCE.
Matashiyar mai suna A'isha Muhammad Lawal ta bayyana cewa ta fara wannan sana'ar tun tana karama, kasancewar ta taso a lokacin yayanta yana yin gyaran kwamfutar wanda a sanadiyyar haka ita ma ta tsinci kanta cikin sana'ar. Sannu a hankali A'isha ta bude shago mallakinta a cikin garin Bauchi. A'isha ta bayyana cewa cikin nasarorin da ta cimma a wannan sana'ar, har da tallafawa kannenta da iyayenta, baya ga dawainiyar kanta da take yi. Sai dai kuma duk da wadannan dimbin nasarori da A'isha ta samu a cikin gyaran kwamfutar da take yi, ta kuma bayyana cewa akwai matsaloli da suke kawo mata tarnaki a cikin harkar. Ahmad Muhammad matashi ne da ke aiki a karkashin A'isha, ya kuma bayyana cewa yana samun kwarewa a cikin sana'ar.