Matashi wanda ke hada na′urar samar da lantarki a Najeriya | Himma dai Matasa | DW | 14.09.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Himma dai Matasa

Matashi wanda ke hada na'urar samar da lantarki a Najeriya

Ahmad Muhammad Sani matashi ne da ya ke hada na’urar samar da wutar lantarki ta hasken rana a unguwar Sharada da ke A Kano,kuma bayan haka yakan kirkiri na’urar kyankyasar kaji,tare da koyar da matasa sana'ar.

La'akari da yawaitar matasa masu zaman banza da kuma irin tarin hadarinsu,a cikin al'umma shi ne makasudin karfafa gwiwar matashin Ahmad Muhd sani,wanda Allah ya bude masa basirar kere-kere ya kuma yi amfani da ita wajen kyautata rayuwar 'yan uwansa matasa.Ahmad ya dai samu wannan fusaha ce a Dubai a lokacin da ya yi zama a can kuma a yanzu ya kan koyar da ita ga matasa a Najeriya.

Wani abu mai karin armashi shi ne furucin shi Ahmad Sani da ya ce hatta jami'ar Bayero ta Kano da makarantun fasaha mallakar gwamnatin Kano suna kawo masa dalibai domin samun ilimi,duk da cewar bai taba samun wani tagomashi koda na godiyya ba daga wata hukuma ta gwamnati.

Sauti da bidiyo akan labarin