Matashi mai taimakon matasa a Kano | Himma dai Matasa | DW | 27.07.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Himma dai Matasa

Matashi mai taimakon matasa a Kano

Sammanin Fatuhu Kantin Kwari haifaffen unguwar Magashi da ke kwaryar birnin Kano a Najeriya na taimakwa matasa da sana'a domin magance zaman banza.

Matashin dankasuwa mai sai da kayan ado na mata, na tallafawa 'yan uwansa matasa a Kano Najeriya

Matashin dankasuwa mai sai da kayan ado na mata, na tallafawa 'yan uwansa matasa a Kano Najeriya

An dai haifi Sammanin Fatuhu a shekarun 1980, kuma bai yi wani karatun boko mai zurfi ba kasancewar tun yana kankani ya taso da sha'awar nema domin dogaro da kai musamman ganin cewar galibin mutanen da ya taso cikinsu a wannan yanki, basu damu da karatun bokon ba kana tsananin kaunar nema domin rufawa kansa da iyayen sa asiri ne ya kara yi masa kaimi wajen bazama neman kudi gadan-gadan tun yana dan kankani. Sammani ya fara neman kudi daga kananan sana'oi na hannu kamar dinkin hula da sayar da gurji da mangwaro da kuma tallan rake, har zuwa shekarar 1997, lokacin da ya koma kasuwar Kantin Kwari a matsayin yaron kanti anan ne ma ya samu sunan nasa na "Sammanin Fatuhu Kantin Kwari," kuma ya ce ya sha wuya matuka. Sai dai kuma duk da wannan wuya da ya sha a iya cewa kwalliya ta biya kudin sabulu domin yanzu haka Sammanin Fatuhu ya zama hamshakin dan kasuwa da ke da sama da mutane 100 a karkashinsa domin wajen neman abinci cikinsu kuwa akwai tsofaffi da matasa maza da mata, Musulmi da ma wadanda ma ba Musulmi ba.

Blessing guda ce daga cikin ma'aikatan da ke aiki a babban kantin Sammanin Fatuhu da ke kan titin zuwa Zariya a Kanon ta kuma bayyana cewa tana jin dadin yin aiki a karkashinsa. Galiban masu kanti a Kano sukan dakile yaransu da hana musu sakewa kana kuma makomar yaran masu kanti ba kasafai take haskakawa ba, idan ba an yi sa a an sami mai kaunar ci gaban matasa kamar Sammanin Fatuhu ba a lafazin Shu'aibu wanda ke zaman manaja a daya daga cikin kantina mallakar Sammanin da ke cikin kasuwar Kantin Kwari.

Bahaushe ya kance idan kaji wane ba banza ba, domin kafin kai wa ga wannan matsayi Sammanin Fatuhu ya sha gwagwarmaya domin kuwa har zaman kurkuku ya taba yi a kan abin da ya shafi kasuwanci. Duk da cewar ya fara kasuwancinsa ne a cikin kasuwar Kantin Kwari yanzu haka ya sake ya fadada kasuwancin nasa, inda yake yin wasu harkokin daban da irin kayan kasuwar ta Kwari. Sammani ya ja hankalin 'yan uwa matasa da su dage da neman na kai da kuma kaucewa shaye-shaye da tayar da tarzoma domin rabon kwado baya hawa sama.

Sauti da bidiyo akan labarin