Matasa sun kashe wani matashi a Kano | Labarai | DW | 16.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Matasa sun kashe wani matashi a Kano

Matasa dake tsaro a babban masallacin Jum'maa na cikin Birnin Kano sun farwa wani matashi da yayi yunkurin shiga harabar masallacin yayin da ake shirin fara salla.

Shaidun gani da ido sun tabbatar da cewar an sami karamar bindiga ne tare da wannan matashi yayinbinciken masu shiga masallacin da ake yi kuma nan take aka fara dukan matashin kafin daga bisani ya arce a guje. Matasan dai dauke da makamai sun bi wannan matashi in da suka galabaitar dashi har rai ya yi halinsa. Wakilinmu na Kanon Nasir Salisu Zango ya ruwaito cewa rundunar 'yan sandan jihar ta Kano ta tabbatar da faruwar wannan al amari sai dai tace bata kammala bincike ba dan haka bazata ce komai ba a kai. Kasa da watanni biyu ke nan da aka kai harin kunar bakin wake a babban masallacin Jumma'ar da ke kusa da fadar mai martaba sarkin na Kano tare da hallaka mutane da dama yayin da wasu suka jikkata, hakan ce ta sanya aka tsaurara matakan tsaro a dukkan masallatan Jumma'a na Kanon.

Mawallafa: Nasir Salisu Zango/Lateefa Ja'afar
Edita: Usman Shehu Usman