1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Kungiyar ECOWAS na son a biya diyyar corona

Uwais Abubakar Idris
March 8, 2021

A kokarin jan hankulan ‘yan Najeriya kan amincewa da allurar rigakafin cutar corona, Kungiyar ECOWAS ta bukaci gwamnati da ta dauki mataki na biyan diyya ga duk wanda ya fuskanci duk wata matsala a sakamakon yin allurar.

https://p.dw.com/p/3qM1j
Nigeria Covid-19 Impfung in Abuja | Dr. Cyprian Ngong
Cyprian Ngong-Likitan farko da aka yi wa allurar rigakafin coronaHoto: Uwais Idriss/DW

A  ci gaba da kokari na janyo hankulan ‘yan Najeriya don su rungumi shirin yin allurar rigakafin cutar corona da aka fara a kasar, Kungiyar gamayyara Kasashen Yammacin Afrika (ECOWAS) ta bukaci kasashen su biya diyyaga duk wanda ya fuskanci wata matsala sakamakon allurar corona. Ko wane tasiri wannan zai yi a kokari na samun karbuwar allurar da kawar da rashin yarda a zukattan wasu daga cikin al'ummar kasa? Wannan ita ce tambayar da jama'ar kasar ke son sanin amsarta. Karin Bayani:  Agajin riga-kafin corona ga Afirka

Ghana ECOWAS | Nana Akufo-Addo
Ecowas na son tsarin biyan diyyaHoto: AFP/N. Dennis

Kwanaki uku da fara allurar rigakafin cutar ta Covid 19 a Najeriyar ne, Kungiyar Ecowas ta bullo da batu na samar da kyakyawan tsari don biyan diyya ga duk wanda ya samu wata matsala sakamakon allurar rigakafin cutar ta Covid 19 a kasashen Afrika ta yamma, sanin cewa Najeriyar ta bi sahun kasar Ghanawajen samu dama fara aiwatar da allurar da ake cike da fata za ta taimaka murkushe wannan annoba da ta girgiza duniya. Tuni dai jami’an kula da lafiya da kungiyoyi  kare hakin jama’a ke bayyana ra'yoyi kan tasirin da wannan zai yi wajen kara cusa yarda da ma tabbatar da kare hakkin duk wanda ya karbi allurar.

Ghana Accra | 37 Militärkrankenhaus: Nana Akufo-Addo wird geimpft
Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo Hoto: Information ministry of Ghana

Sanin cewa har yanzu kasashen Afrikan sun dogara ne a kan samar masu da allurar cutar ta Covid 19 abin da ke sanya daga 'yar yatsa. Ministan Lafiya a Najeriyar Dr Osagie Ehanire ya bayyana matakan da aka samar domin tabbatar da babu batu na jabun alluran rigkafin a Najeriya yana mai cewa. ‘’Ya ce duk wata allurar rigakafin da bata samu amincewar hukuma kula da inganci abinci da magunguna ta Najeriya ba, to an dauketa tana da hatsari kuma jami’an hukumar da na kwastom za su sa ido, tuni akwai allurarar corona na jabu a kasuwanin duniya, gwamnatin Najeriya a shirye take da biyan dukkanin bukatu a wannan fani'' Bullo da biyan diyya ga wadanda allurar ta corona za ta yi wa illa dai babban mataki ne da zai kawar da yanayi na dar-dar da ake fama a sassan Najeriyar.