1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Diyya a sakamakon illar riga-kafin corona

Ramatu Garba Baba
February 22, 2021

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta amince da biyan diyya ga duk wadan ya sami matsala bayan an yi masa allurar riga kafin corona. Shirin ya shafi kasashe kimanin 92 da ke fama da matsanancin talauci.

https://p.dw.com/p/3piz2
BG "Die Welt im Griff von Corona"
Hoto: Rodger Bosch/AFP/Getty Images

Biyan diyyar ya danganta ga wadanda aka yi wa allurar a karkashin shirin samar da magani na Covax. Lamarin da ake ganin ka iya kawar da shakku a tsakanin jama'a dama gwamnatoci a game da illolin da ake fargabar allurar rigakafin cutar mai kama numfashi na iya haifarwa.

A daya bangaren kuwa, wani bincike na masana da aka gudanar a Britaniya, ya nuna yadda aka samu raguwar yaduwar cutar corona saboda tasirin allurar rigakafin, wanda ke nufin zai matukar yin tasiri a sauran kasashen duniya, muddun aka rungumi tsarin yi wa al'umma allurar riga-kafin cutar.

A yankin Turai kuwa, gwamnatin kasar Italiya ta kara tsawaita dokar hana shige da fice a tsakanin kasar da sauran kasashe na yankin Turai. Sabuwar gwamnatin Firaiminista Mario Draghi, ta ce ta dauki matakin ne don shawo kan annobar corona da ke ci gaba da yaduwa a sassan kasar. Kasar ta ce za ta ci gaba da dokar kulle har ya zuwa ranar 27 ga watan Maris.