Matakin bai daya kan ′yan gudun hijira | Labarai | DW | 24.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Matakin bai daya kan 'yan gudun hijira

Shugabannin Faransa da Jamus sun yi kira ga takwarorinsu na Turai da su dauki matakin bai daya don tallafawa masu gudun hijira.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da shugaban kasar Faransa Francois Hollande sun yi kira ga takwarorinsu na Turai da su dauki mataki na bai daya wajen tinkarar matsalar 'yan gudun hijiran da nahiyar ke fiskanta, abin da suka kira mafi tsanani tun bayan yakin duniya na II.

Merkel wacce kasarta ke sa ran 'yan gudun hijira dubu 800 ne za su sami mafaka, ta ce Jamus da Faransa na fatan ganin duk kasashen Turai sun mutunta tanadin manufofin kungiyar nan ba da dadewa ba.

Haka nan kuma, ta kara da cewa Jamus da Faransa, sun amince da matakin zana sunayen kasashen da ya kamata a baiwa 'yan gudun hijiransu mafaka. Jamus ta dade tana hankoron ganin an fara amfani da wannan manufa a hukumance ganin cewa mafi yawan masu gudun hijirar da ke zuwa kasarta daga yankin Balkan ne.