Matakan tsaro a Slovakia gabanin taron EU | Labarai | DW | 12.08.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Matakan tsaro a Slovakia gabanin taron EU

Kasar Slovakia ta bayyana cewa ta tsaurara matakan tsaronta a filayen tashi da saukar jiragen sama a ranar Juma'an nan , bayan bazuwar wasu sakonni na barazana cewar za a kai hare-hare kafin taron EU.

Brüssel EU-Ratspräsident Donald Tusk

Donald Tusk Shugaban Kungiyar EU

Ivan Netik da ke magana da yawun ma'aikatar harkokin cikin gida ya bayyana cewa an tsaurara matakan tsaron ne a filayen tashi da saukar jiragen sama na Bratislava da Poprad da Kosice.

Kungiyar ta EU dai ta tsara babban taron kolinta za a yi a birnin Bratislava da ke zama babban birnin kasar ta Slovakia a ranar 16 ga watan Satimba inda za a tattauna kan makomar kungiyar bayan da Birtaniya ta zabi ficewa a watan Yuni.