Matakan soji a matsayin zabi na gaba don magance rikicin Siriya | Labarai | DW | 23.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Matakan soji a matsayin zabi na gaba don magance rikicin Siriya

Amirka ta ce a shirye take domin tinkarar magance matsalar kungiyar IS idan duk kokarin kawo karshen rikicin cikin lumana ya gagara.

Mataimakin shugaban kasar Amirka Joe Biden ya jaddada cewar kasashen Amirka da Turkiyya a shirye suke domin daukar matakin soji a matsayin hanyar magance ayyukan ta'addanci gami da yakar kungiyar IS a Siriya a duk lokacin da gwamnatin kasar da 'yan tawaye suka gaza wajen samun maslahar siyasar kasar.

Joe Biden ya furta kalaman ne a wani taron manema labarai da suka gudanar tare da Firaministan Turkiyya Ahmet Davutoglu a birnin Istanbul na kasar Turkiyya a dai-dai lokacin da ake shirye-shiryen fara wata tattaunawar zaman lafiyar Siriyan a birnin Geneva a ranar Litinin mai zuwa.

Ya ce: "Ko tantama babu a shirye muke a kan wannan matakin, John Kerry yana ganawa da mahukuntan Saudiyya a dai-dai lokacin da muke wannan maganar, kana za mu gana a birnin Davos a inda Firaminista da ni muka gana da takwarorinmu."

Kazalika Biden ya kara da cewar shi da Firaminista Ahmed Davutoglu sun tattauna a kan yadda za su tallafa wa 'yan tawayen da ke fafutukar ganin sun kawar da shugaba Bashar Al-Assad daga mulki.