1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arziki

Najeriya: Cece-kuce kan matakan CBN

Lateefa Mustapha Ja'afar
December 9, 2022

Matakin babban bankin Najeriya CBN, na takaita yawan kudin da mutum zai iya cira a asusun bankinsa na ajiya na ci gaba da jawo martani da fargaba a tsakanin masana da sauran al'ummar kasar.

https://p.dw.com/p/4KkDl
Najeriya | Naira | Banki
Matakin sabunta kudi da kayyade adadin da mutum zai iya dauka a bankinsa a NajeriyaHoto: Ubale Musa/DW

Da yawan mutane musmaman a arewacin Najeriyar sun fi sha'awar ajiye kudinsu a gida, a dangane da haka suke kallon wnanan doka a matsayin wani sabon salo da zai tagayyara tattalin arzikinsu. A hannu guda kuma ba wai talakawa da kananan 'yan kasuwa ne kadai ke yin korafi kan wannan sabuwar doka ba, domin kuwa a wani abu mai kama da alamun raba gari a tsakanin majalisar dokokin Najeriyar da bangaren zartarwa majalisun kasar guda biyu sun nemi dakatar da sabon shirin sauyin fasalin harkokin kudin.

Tun ba a kai ga ko'ina ba dai zuciya ta fara tafasa a bangaren 'yan bokon Najeriyar da ke adawa da sabon tsarin tafiyar da kudin kasar da babban bankin na CBN ya fitar. Majalisun tarrayar guda biyu da tuni suka aike sammaci ga gwamnan babban banki dai, sun ce ba za su amince a jefa kasar cikin rudani da sunan zamanantar da harkar hada-hadar kudi ba.

Ba wai kawai babbar jam'iyyar adawa ta PDP ce ke kalubalantar matakin CBN din ba, har ma da APC mai mulki, a tsakanin 'yan dokar da zuciyar su ke tafasa kan manufofin yin adabo da takardun kudin da ke zaman makamashin siyasar Najeriyar. A ranar Alhamis din makon gobe ne dai, aka tsara gwamnan babban bankin Najeriyar Godwin Emefiele zai bayyana a gaban 'yan dokar, a cikin jan aikin shawo kai da kila sauya tunani na da dama da ke fatan amfani da kudin a zabukan kasar na badi.