Matakan bunkasa abinci | BATUTUWA | DW | 16.10.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Matakan bunkasa abinci

16 ga watan Oktoba, rana ce da Majalisar Dinkin Duniya ta kebe domin nazarin wadatar abinci a duniya baki daya. Manufar wannan rana ta hada da yaki da yunwa. Jihar Bauchi da ke arewacin Najeriya an samu ci-gaba.

Shirin Fadama, shiri ne da gwamnatin Jihar Bauchi ta bullo da shi da nufin samar da wadataccen abinci ga mutanen jihar kasancewar a baya akwai tsofaffin hanyoyi da ake amfani da su saboda samar da abinci wadanda a yanzu kuma zamani ya chanja wanda hakan ke nufin neman wasu sababbin hanyoyin samar da abinci. Wannan na daga cikin dalilan samar da wannan shirin a jihar inda tuni ya yi nisa har ya kai ga mataki na uku.

Tuni dai jama'a musamman manoma suka rungumi wannan shiri na Fadama inda kuma zuwa yanzu za a iya cewa kwalliya ta biya kudin sabulu ta fuskar samun abinci a wadace a jihar sabanin yadda a baya jama'ar jihar ta Bauchi suke fama da karancin abinci kamar yadda Hassan Jibrin Rimi wani manomin rani wanda ya samu cin gajiyar shirin ya shaida mana.

Taken bikin ranar abinci ta duniyar a bana dai shi ne kawar da yunwa a tsakanin al'umma wanda kuma na daga cikin manufar hukumar abinci ta Majalisar Dinkin Duniya a shekara ta 2030, hukumar tana fatan ganin an fatattaki yunwa a tsakanin al'umma musamman marasa karfi.

Sauti da bidiyo akan labarin