1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bauchi: Mataimakin gwamna ya ajiye aiki

Aliyu Muhammad Waziri AS
May 24, 2018

A daren ranar Laraba ce mataimakin gwamnan jihar Bauchi Injiniya Nuhu Gidado ya yi murabus daga mukaminsa bayan da ya mika takardar barin aiki ga gwamnan jihar Bauchin Muhammad Abdullahi Abubakar. 

https://p.dw.com/p/2yGyQ
10.03.2013 DW online Karten Karussell Nigeria Abuja Bauchi

Bayanai sun yi nuni da cewa tun a watan Afrilun da ya gabata ne mataikamakin gwmanan ya bayyana wa gwamnan kudirin sa na ajiye aiki amma sai yanzu lokaci ya yi. Injiniya Nuhu Gidado ya ce ya yi murabus din ne bisa dalilin rashin gamsuwa da yadda lamura suke tafiya karakashin jagorancin gwamna Muhammad Abdullahi Abubakar.

To ko ina matsayin gwamnatin jihar Bauchi kan wannan labari, Kwamared Sabo Muhammad shi ne mai tallafa wa gwamnan jiha kan harkokin ilimi da wayar da kan jama'a, yace ai da ma kaddara ta riga fata. Jama'a da dama dai na ganin cewa murabus din mataimakin gwaman na iya tasiri wajen kawo koma-baya ga kokarin gwamnan na sake komawa wa'adi na biyu.

Wannan lamari na zuwa ne a dai-dai loakcin da rikicin cikin gida a jam'iyyar APC a Bauchi ke kara ta'azzara tsakanin ya'yan jam'iyyar wanda har ma wasu daga cikin manyan jiga-jigan jam'iyyar ke bayyana tafiyar da rashin adalci. Murabus din Injiniya Gidado dai ta shiga tarihi a dandamalin siyasar Najeriya kasancewa tun dawowa tafarkin damokuradiyyar kasar a shekarar 1999 ba'a taba samun wani gwamna ko mataimakin sa da ya ajiye mukamin sa bisa radin kai.