Masu sa ido sun yaba da zaben Madagaska | Labarai | DW | 27.10.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Masu sa ido sun yaba da zaben Madagaska

Zaben na ranar Juma'a na zama irinsa na farko tun bayan kifar da gwamnatin Marc Ravolamanana a shekara ta 2009, daga nan ne kasar ta fada matsalar tattalin arziki.

Masu sanya idanu a harkokin zabe, sun yaba da yadda aka gudanar da zaben shugaban kasa, a ranar Juma'a a kasar Madagaska, a daidai lokacin da ake hasashen yiwuwar zuwa zagaye na biyu. Wakilan Kungiyar Tarayyar Turai EU da na Kungiyar Kasashen kudancin Afirka ta SADC, sun bayyana cewar, zaben ya gudana cikin lumana da adalci ba tare da wani magudi ba. Ana sa ran zaben na ranar Juma'a ya kawo karshen matsalolin siyasa da tattalin arziki na shekaru hudu da kasar ke fama da su tun bayan kifar da gwamnati a wannan kasar Afirka da ke tsibirin Indiya a shekara ta 2009. Bayan kidayar kashi 11 daga cikin 100 na yawan kuri'u da aka kada dai, magoya bayan hambararren shugaban kasa Marc Ravalomanana da na abokin takararsa kuma shugaba mai barin gado Andry Rajoelina, na ganin cewar sakamakonsu na tafiya kafada da kafada, wanda zai iya kai su zagaye na biyu na zaben shugaban kasar a watan Disamba.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Mohammad Nasiru Awal