1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Masu kutsen komfutoci sun nemi kudin fansa

Ramatu Garba Baba
July 5, 2021

Wadanda ake zargi da kutsen komfutoci na manyan kasashen duniya ne suka nemi da a biya su dala miliyan 70 a matsayin kudin fansa kafin su bayar da hadin kai.

https://p.dw.com/p/3w3Tv
Symbolbild Hackerangriff
Hoto: Nicolas Asfouri/AFP/Getty Images

Wasu gungun mashahuran da ake zargi da badakalar kusten komfutocin a kasashen duniya, sun bukaci a biya su dala miliyan saba'in a matsayin kudin fansa kafin su saki shafukan da sauran bayanan da suka kwace. 

Mutanen da ake zargi da laifuka na kustawa cikin rumbunan bayanan sirrin kamfanoni a sassan duniyan, sun shigar da wannan bukatar ta hanyar wallafa sakon ne a shafinsu, wanda tuni masu aikin binciken lamarin, suka tabbatar da sahihancinsa.

Al'amura sun tsaya cik, inda kamfanoni da dama suka gagara yin mu'amala ta kudi yayin da wasu suka koma amfani da tsohuwar hanyar fax da wayar tarho, Amirka da kasashen Turai lamarin ya fi shafa.