Martanin Nijar bayan yakin Faransa da ′yan kungiyar AQMI | Siyasa | DW | 13.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Martanin Nijar bayan yakin Faransa da 'yan kungiyar AQMI

Faransa tace ta kwace makama daga hannun 'yan kungiyar AQMI sakamakon yakin da suka yi a yankin hamadar kasar Nijar a tsakiyar makon jiya.

A jamhuriyar Nijar wasu yan kasar ne su ka soma mayar da martani dangane da aikin da sojojin kasar Faransa da ke girke a cikin yankin Sahara na kasar ta Nijar suka na fatattakar wani ayarin motocin kungiyar mayakan jihadi ta AQMI shake da manyan makammai a cikin yankin Saharar kasar ta Nijar. Saidai a yayin da wasu yan Nijar din ke yabawa aikin da sojojin Fararnsar su ka yi, wasu na ganin duk da haka zamansu a Nijar ba alkhairi ba ne.

A daren Alhamis, washegarin ranar Juma'ar da ta gabata ne sojojin
kasar Faransa wadanda ke aikin tabbatar da tsaro a cikin yankin
Saharar Nijar su ka yi nasarar murkushe wani ayarin motoci makare da manyan makamai da mayakan kungiyar yan jihadi ta AQMI su ka kwaso daga kasar Libiya zuwa kasar Mali. Sanarwar fadar shugaban kasar Faransar wacce tace aikin ya wakana ne da hadin bakin hukumomin kasar Nijar, ta kara da cewar sojin Faransar sun yi nasarar kama makamai da dama, da ma wasu daga cikin mayakan kungiyar ta AQMI. Sai dai kuma bata ambato ko an samu mutuwa ko jimuwa a cikin artabun ba. Yau watanni da dama kenan dai dama da sojojin kasar Faransa wadanda ke aiki a karkashin inwar rundunar tsaro ta Barkan ke girke a cikin yankin Saharar Nijar. Kuma a wancan lokaci yan Nijar da dama ne suka nuna adawarsu da shirin, wanda suke gani a matsayin wani sabon mulkin mallaka. To amma a halin yanzu wasu yan Nijar na ganin zaman sojin Faransar a Nijar ya soma zama alkhairi ko da yake sun ce Faransar ta makaro.

Saidai a daidai lokacin da wasu ke nuna gamsuwarsu da aikin sojojin
kasar Faransar a cikin kasar Nijar wasu na ganin akasin haka. Malam
Nuhu Arzika, shugaban kawancen kungiyoyin farar hula na MPNCR, na daga cikin masu adawa tun farko da zaman sojojin Faransar a Nijar kuma ya ce ko a yanzu suna nan a kan bakansu.

Niger Präsident Mahamadou Issoufou

Shugaban Nijar, Mahamadou Issoufou

Shi ko Malam Sani, wani mazaunin birnin Yamai cewa ya yi ko da yake
aikin da sojojin Faransar suka yi abin yabawa ne, to amma bai kamata ba
su ci gaba da zama a cikin kasar ta Nijar domin hakan na iya jawo
hushin kungiyoyin 'yan jihadin ga kasar ta Nijar.

Sai dai Har kawo yanzu dai babu wata sanarwa daga bangaren gwamnati, ko
kuma hukumomin sojin Nijar dangane da wannan labari, wanda fadar
shugaban kasar Faransa ce ta bada shi ga duniya.

Sauti da bidiyo akan labarin