Martanin Najeriya kan tauyen hakkin bani Adama | Siyasa | DW | 26.02.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Martanin Najeriya kan tauyen hakkin bani Adama

Gwamnatin Najeriya ta ce kungiyar Amnesty International ta saba zargin sojojinta da laifin take hakkokin bani Adama. Sai dai kuma ba Najeriya kadai ce kasar da kungiyar IS ke daukar magoya bayanta ba.

Batutuwa na rashin tsaro da nasarorin da Najeriyar ke bayyanawa cewa ta na samu a yaki da masu kai hare-hare a yankin Arewa maso gabashin kasar ne suka dauki hankalin cibayar samar da bayanai a kan ayyukan ta'adanci. Wannan ba ya rasa nasaba da rahoton da Amnesty International ta fitar wanda a fili ya soki jami'an tsaron Najeriyar da laifuffukan take hakkin jama'a da ma azabtar da fararen hula da suke kamawa. Mike Omeri, shugaban wannan cibiyar ya nuna tababa a kan wannan zargi, amma ya ce za su bincika.

Nigeria Kampf gegen Boko Haram Islamisten

Sojojin Najeriya ba sa sara tare da duban bakin gatari

‘'Amnesty Internatioanl ta sha yin irin wannan zargi kuma bayanai da aka bayar da shi ne har yanzu , amma duk inda irin wannan zargi ya fito ana bincikawa a kan hakan,. Kuma ana hukunta duk wanda aka gani ya na kokarin cin zarfain dan kasa da ke son zaman lafiya. ''

Kungiyar Amnesty International ta kuma gargadi Najeriyar a kan yadda ake samun yawaitar amfani da hanyar sadarwa ta internet wajen jirkita hallayar matasa su kangare, abinda ke sa su shiga kungiyoyin da ke tada kayar baya. Mike Omeri ya ce wannan gaskiya ne. Sai dai ‘'Bincike na jami'an tsaro ya nuna cewa ba Najeriya kadai ba ne ake yin wannan don a jawo yara a cikin irin wannan halin. Abinda Isis suke yi ai bashi da bambanci da abinda Boko Haram ke yi.''

DW_Nigeria_Integration-online3

Al'ummar arewacin Najeriya sun shiga cikin mawuyacin hali

Najeriyar dai na mai bayyana ci gaba da samun nasarori a yaki da ta'addanci musamman ta fannin karbo garuruwan da suka subuce daga ikon gwamnati. To sai dai ta na ci gaba da fuskantar samun kai hare-hare a yanayi na sari-ka-noke na zama wani sabon kalubale baya ga garkuwa da ma sace mutane da ake yi.

Sauti da bidiyo akan labarin