1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martanin kama 'yan Boko Haram

Uwais Abubakar Idris
July 19, 2018

A Najeriya ana maida martani a kan kame mutane takwas da rundunar ‘yan sandan ta yi bisa zarginsu da hannu wajen sace ‘yan matan Chibok da ya faru shekaru hudu da rabi kenan

https://p.dw.com/p/31lb8
Nigeria Symbolbild Korruption
Hoto: picture alliance/NurPhoto

To kame mutanen takwas tare da gabatar da su a gaban jama’a bisa zargin 'ya'yan kungiyar ta Boko Haram da suka kitsa sace ‘yan matan na Chibok, na zama wanda ya samar da sabuwar fata musamman ga iyayen yaran da ma masu fafitika na ganin an kai ga sako saurarn ‘yan matan da har yanzu ake tsare da su.

Fatar da ake da ita ba kawai ta kai wa ga gano sauran ‘yan matan ba, amma warware zare da abawar abin da ya faru, kuma su wa-da- wa suke da hannu a yanayi na kama hanyar alura na iya tono garma. Mr Hosea Tsambido Abana, jigo ne a kungiyar al'ummar Chibok da ke Abuja kana manmba a kungiyar ta Bring Back Our Girls. Wanda ya bayyanan farin ciki da wannan labarin.

Nigeria Demonstration Bring Back Our Girls in Chibok
Hoto: Reuters/A. Akinleye

Batun ‘yan matan na Chibok da aka sace su a ranar 14 ga watan Yulin shekara ta 2014, na zama wanda ke daukar hankali sosai, abin da ya sanya gabatar da mutanen da ake zargi ya zama muhimmi a kasar. To sai dai ga Mallam Dantata Mahmud, na kungiyar tsaro da wanzar da zaman lafiya a yankin arewa, ya ce akwai darasi abin koyi ga kaiwa ga kame mutanen da ake zargi fiye da shekaru hudu bayan aikata laifin.

Wannan dai shi ne karo na biyu da ake kame mutanen da ake zargin suna da hannu a kan zargin sace ‘yan matan na Chibok. Masu fafutuka da ma iyayen ‘yan matan za su zura ido don ganin abin da zai biyo baya, tare da tsoron kada ya zama a ji shiru a kan lamarin.