Muna amfani da "Cookies" domin inganta abubuwan da muke wallafawa a intanet. Za ku iya samun karin bayani a kundin kare bayananmu.
Ana cigaba da samun martani daga ciki da wajen Najeriya dangane da sauke Sarki Muhammadu Sanusi na biyu da gwamnatin jihar Kano a karkashin Abdullahi Umar Ganduje ta yi.
Kungiyar Amnesty International mai fafutukar kare hakkin bil'adama ta nemi hukumomin tarrayar Najeriya da su mutunta 'yancin tsohon sarkin Kano da aka mayar garin Awe a jihar Nasarawa. (11.03.2020)
A Najeriya ana ci gaba da mayar da martani biyo bayan tsige mai martaba Sanusi Lamido Sanusi a matsayin sarkin Kano da gwamnatin jihar ta yi bayan shafe tsawon lokaci ana sa-in-sa a tsakanin sarkin da gwamnan jihar. (10.03.2020)
Bayan da gwamnatin jihar Kano da ake arewacin Najeriya ta tube Sarki Muhammadu Sanusi II, yanzu haka an nada Aminu Ado Bayero a matsayin sabon Sarkin Kano. (09.03.2020)
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kai ziyarar kaddamar da ayyuka a jihar Kano, ziyarar da aka shawarce shi ya dakatar da ita saboda fargabar abin da ya faru yayin makamanciyarta a jihar Katsina amma ya ce ba fashi.