Martani kan karin mafi karancin albashi a Najeriya | Siyasa | DW | 19.04.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Martani kan karin mafi karancin albashi a Najeriya

Bayan sabon mafi karancin albashi a cikin Najeriya inda tsallen murna na zaman karatun ma'aikatan kasar dake kallon damar rage radadi na talauci sakamakon karin da ke zaman na farko a lokaci mai tazara.

Sun dai dauki shekaru dai dai har guda Biyu suna fafutuka, sannan kuma sun kai ga zanga zanga dama barazana ta yajion aiki, kafin kaiwa ga tilasta gwamnatin ta Abuja karin albashin a karon farko cikin tsawon shekaru kusan 10.

Babu dai zato ba kuma tsamani wata sanarwar fadar gwamnatin kasar ta tabbatar da rattaba hannu kan Naira 30,000 a matsayin mafi karancin albashi ga daukacin ma'aikatan da ke aiki a kasar.

Wannan doka ta tilasta duk wani mai daukar aiki a tarrayar Najeriya da ya biya  Naira 30,000 a matsayin mafi karancin albashi, to sai dai wannan bai shafi wadanda ke daukar aikin da bai kai mutane 25 ba da kuma wanda suke aikin karba-karba, da kuma ragowar da ke cikin wani tsari na daban da dokar ta amince da shi.

Kafin dokar dai mafi karancin albashi a cikin Najeriya na zaman Naira 18,000 adadin kuma da ke zaman mafi karanci a daukacin yankin yammacin Afirka.

Duk da cewar dai sabon Karin ya fara aiki nan take babban kalubale ga ma'aikata musamman a jihohi da kananan hukumomi na zaman iya kai wa ga biyan hakkokin ma'aikatan a kan kari.

Sauti da bidiyo akan labarin