Martani kan kara dakarun Faransa a Afirka | Siyasa | DW | 12.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Martani kan kara dakarun Faransa a Afirka

Tun bayan da gwamnatin Faransa ta sanar da manufarta na tura karin dakaru zuwa yammacin Afirka domin yakar Boko Haram ne dai, mahawara ta kunno kai a Nijar.

A Jamhuriyar Nijar, masana da ma kungiyoyin kare hakkin jama'a na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu kan yiwuwar karin dakarun kasar Faransa a kasashen Afirka, musamman ma a Nijar domin yaki da 'yan Boko Haram.

Ra'ayoyi dai sun banbanta kan kafa rundunonin na Faransa. A yayin da wasu ke yabawa da kokarin da sojojin ke yi, wasu kuwa na mai kallon batun tamkar wani sabon salo ne na mulkin mallaka.

Tun a farkon wannan shekarar ce dai sojojin Kamaru da Chadi da Nijar da kuma Benin, suka fara taimaka wa takwarorinsu na Najeriya a kokarinsu na kawo karshen mayakan tada kayar baya na Boko Haram, bayan da kungiyar ta karbe madafan ikon wasu yankunan kasar, tare da fara kaddamar da hare-hare a kan garuruwan da ke kan iyakokin kasashe makwabta.

A yanzu haka dai Faransa na da adadin sojojinta 3,000 a yankin, ban da wasu dakaru na musamman, wadanda ke jibge a Mauritaniya daga yammaci zuwa kudancin Libiya, wadanda aka dora wa alhakin farautar mayakan kungiyar Al-qaida.

Sauti da bidiyo akan labarin