Martani gida da waje kan makomar Mugabe | Siyasa | DW | 22.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Martani gida da waje kan makomar Mugabe

Kasashen duniya na bayyana martani game da murabus din Shugaba Robert Mugabe daga karagar mulkin kasar Zimbabuwe bisa matsin lambar sojoji da ma sauran al'ummar kasar.

Kwana daya bayan da kasar Zimbabuwe ta bude sabon babin rayuwa bayan shekaru 37 na mulkin Mugabe yanzu haka kasashe da kungiyoyin kasa da kasa su na tofa albarakcin bakinsu dangane da yadda mulkin Mugabe ya kawo karshe da kuma makomar kasar a nan gaba. Kasar Birtaniya ta bakin sakataren harakokin wajenta Boris Johnson fatan kyakkyawar makoma ya yi ga kasar wacce ya ce za su zura ido su ga abin da zai biyo baya daga yanzu:

Großbritannien Boris Johnson in Manchester (picture-alliance/dpa/O. Humphreys)

Birtaniya uwargijiya ta Zimbabuwe ta yi murna da saukar Mugabe ba tare da zubar jini ba

"Za mu zura ido mu ga yadda al'amura za su kasance a nan gaba a kasar, amma dai ga alama za a iya cewa lokaci ne na farin ciki da fata ga kasar. Yanzu sauyi ya samu inda za su iya tsayawa takara a zaben da za a shirya a kasar a shekara mai kamawa, wanda muke goyan bayansa, tare da sauran kasashen yankin."

Ita ma dai kasar Amirka ta yaba da yadda aka samu sauyi a kasar ta Zimbabuwe ta hanyar demokradiyya ba tare da zubar da jinin 'yan kasa ba. A cikin wata hira da ta yi da manema labarai kan batun kasar ta Zimbabuwe Heather Nauert mai magana da yawun ofishin ministan harkokin wajen kasar ta Amirka, bayyana lamarin ta yi da wani babban abin tarihi ga kasar ta Zimbabuwe inda ta yi karin bayani:

"Saukar Mugabe daga mulki wani babban abin tarihi ne kuma wata babbar dama ce ga al'ummar kasar ta bude sabon babin tarihinta. Lalle al'ummar Zimbabuwe ta nuna bukatar kawo karshen zama saniyar ware da kasarsu take ciki. Amma kuma al'ummar kasar ce ke da wuka da nama a yanzu a game da makomar kasarsu."

BG Mugabe, First Lady Grace chat with Chinese Ambassador to Zimbabwe Qi Shunkang, 2012 (picture-alliance/Photoshot/Li Ping)

China da Zimbabuwe na zaman abokan hulda

Ita kuwa kasar Chaina wacce ke zama babbar kawar kasar ta Zimbabuwe a lokacin mulkin Shugaba Mugabe, jinjina wa tsohon shugaban ta yi wanda ta bayyana a matsayin babban amininta. Sai dai wata babbar ayar tambaya ita ce makomar shugaba Mugabe a nan gaba. Tuni dai wasu suka fara batun yiwuwar komawarsa da zama a kasar Afirka ta Kudu. To sai dai Joy Mabenga jagoran kungiyoyin da ke sa ido kan rikicin siyasar kasar ta Zimbabuwe ya ce komawarsa wasu kasashen na nesa ita za ta fi kasancewa alkhairi gare shi.

 

Sauti da bidiyo akan labarin