Manyan abubuwan da suka faru a Najeriya a 2019 | BATUTUWA | DW | 31.12.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Manyan abubuwan da suka faru a Najeriya a 2019

Sa'o'i kalilan da karewar shekara ta 2019, tuni hankali cikin tarrayar Najeriya ya fara karkkata zuwa ga shekarar 2020 da ke shirin shiga kuma mai tasiri ga 'yan kasar.

Präsident Buhari steht dem FEC vor

Zauren taro na fadar gwamnatin Najeriya da ke Abuja

Batun siyasa da tsaro da tattalin arziki dai na zama na kan gaba a shekarar 2019 a Najeriya, kasar da ta kai ga zabukan tarrayar cikin halin rashin tsaro da ma matsi na tattali na arziki.

To sai dai kuma daga dukkan alamu batun siyasa da tsaro ne dai ke neman sake mamaye harkoki a cikin Najeriyar a sabuwar sheakarar 2020.

Duk da cewar dai kasar tana da ragowar shekaru har guda Uku tsakaninta da sabon zabe, tuni dai batu na magaji ga shugaban kasar ya fara daukar hankali a tsakanin manyan jam'iyyun kasar guda Biyu.

Kama daga APC ‘yar mulki ya  zuwa ita kanta PDP ta adawa dai tuni har an fara  nuna alamunin daukar zafi a kokari na dorawa zuwa mataki na gaba na shugabancin kasar a fadar Faruk B.B Faruk da ke zaman wani masani na siyasa a jami'ar babban birnin tarraya ta Abuja.

“Tun yanzu mun ji shugaban dattawan jam'iyyar PDP Walid Jibrin, ya ce sun fara tunanin wa za su ba takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, tun ma kafin wannan shekarar ta fita. Ina tabbatar maka tsakanin jam'iyyar APC da PDP za a fara takun saka a tsakanin wane ne zai fito, wa za a ba, waye ba za a ba ba.”

To sai dai kuma in har shugaban kasar yana neman hanyar kauce wa siyasa, daga dukkan alamu yana da jan aiki ga dan uwansa na tsaro da ya nemi tasiri har ga siyasar ya kuma kai ga tsayuwar lamura a cikin tarrayar Najeriyar a shekarar da ke karewa.

 

Ya zuwa yanzu dai ana samun bambancin ra'ayi a tsakanin hafsoshi na tsaron kasar da ke fadin suna samun nasara da kuma ‘yan kasar da ke ganin daban.

Kuma a fadar Flight Lieutenant Aliko El Rashid da ke sharhi kan tsaro, akwai bukatar sauyin rawa ga tarrayar Najeriyar da ke fatan kai karshen yaki na ta'addanci a shekarar da ke shiga. Batun na tsaro ne dai ya kai ga tarrayar najeriyar Mi'ara koma baya ga tattali na arzikin kasar da ma zamantakewar al'ummarta.

Ita kanta gwamnatin kasar dai ta ambato tsaron cikin hujjar rufe iyakar da ke tsakani da makwabta, kuma a fadar Yusha'u Aliyu da ke zaman masani na tattalin arzikin babu alamun sauyi a shekarar da ke tafe.

To sai dai kuma in har tarrayar Najeriyar na shirin ganin daban ga batun na tattali na arziki, akwai alamun sauyi ga mutunci na dan Adam bayan jeri na zanga zanga dama karin matsin lamba a matakin tarayya.

 

 

Isa Sunusi dai na zaman kakaki na kungiyar Amnesty International mai fafutukar kare hakki na dan adam a tarrayar Najeriyar da ma waje.

“Idan aka yi la'akari da sakin wadannan mutane biyu Omoyele Sowore da Sambo Dasuki  za mu iya cewa akwai alamar cewa gwamnati na shiri ta saurari jama'a, za kuma mu yi mata kyakyawan fata cewa in an shiga sabuwar shekara abubuwa na iya sauyawa. Amma kuma ka sani ba tarrayar bace kawai  misali in kaje jihar Cross River, akwai dan jarida da aka rike shi. Haka a jihar Akwa Ibom akwai wani da ya rubutu a Facebook gwamnan jihar ya sa aka rufe shi. Abin da yake faruwa a jihohi ma ya fi hatsari.”

Milliyoyin al'umma na kasar dai na fatan su ga sauyin rayuwa cikin Najeriyar da ke ikirarin zama ta kan gaba a nahiyar Afirka, amma kuma  al'ummarta ke ji  har a kwakwalwa.

Sauti da bidiyo akan labarin