1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Ko za a magance cin-hanci?

Uwais Abubakar Idris LMJ
July 14, 2022

A ci gaba da kokari na tona asirin masu cin hanci da rashawa a Najeriya, an kadammar da wata sabuwar manhaja da za ta bayar da dama ga ‘yan kasar su yi tonon silili ga masu aikata wannan mumunan dabi’a.

https://p.dw.com/p/4E9O6
Najeriya | Manhaja | Cin-Hanci
Sabuawar manhajar gano masu cin-hanci a Najeriya daga hukumar EFCCHoto: Uwais Abubakar Idris/DW

A tsanake ne dai aka samar da wannan manhaja da aka yi wa lakabi da CORA, wacce cikin sauki ake son 'yan Najeriya su rungumi yaki da cin-hanci da rashawa ta hanyar amfani da internet a matsayin tasu gudummawar. Samar da manhajar da za a iya amfani da ita ta amfani da internet dai, abu ne da ake hasashen zai taimaka sosai. Shekaru shida kenan da Najeriyar ta bullo da tsarin tonon silili, amma sai ya zama wanda ya yi tashi na kumfar sabulu lokaci daya ya dushe saboda matsaloli na rashin kariya ga wadanda suka yi kwarmaton. Tun kafin wannan lokaci dai Hukumar Yaki da Cin-hanci da Rashawa ta kasar EFCC, ta fitar da irin wannan manhaja. Cin-hanci da rashawa babbar matsala ce ga Najeriya a matsayinta na kasa, inda sai dai hasashe na yawan kudin da ake ci gaba da sacewa da ke jefa rayuwar al'umma cikin mawuyacin hali duk da matakai da ake ikirarin dauka.