1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mali na son Faransa ta fice cikin gaggawa

Mouhamadou Awal Balarabe
February 18, 2022

Gwamnatin mulkin soji ta mali ta bukaci Faransa da ta janye sojojinta ba tare da bata lokaci ba daga kasarta, kwana guda bayan sanarwar da Paris da kawayenta suka yi na janyewa cikin 'yan watanni masu zuwa.

https://p.dw.com/p/47GAz
Französischen Marine-Spezialeinheiten bildet in Mali aus
Hoto: Thomas Coex/AFP/Getty Images

A cikin wata sanarwa da aka karanta a gidan talabijin na kasar, mai magana da yawun gwamnatin sojin Mali Kanar Abdoulaye Maïga, ya ce matakin da Faransa ta dauka na janyewa ya saba wa yarjejeniya da aka kulla tsakanin kasashen biyu. Sannan ya kara da cewa kwalliyar Faransa ba ta biya kudin sabulu ba bayan shekaru tara na yaki da ta'adanci a Mali ba, saboda ta janye ba tare da bata lokaci ba.

Sai dai Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya yi watsi da bukatar ta janye sojojin cikin gaggwa daga Mali, tare da yin gargadi kan duk wata barazana ga tsaron lafiyarsu. A yayin wani taron manema labarai bayan taron koli tsakanin kungiyar EU da AU ta Tarayyar Afirka a Brussels, Macron ya ce za su yi amfani da  kyakkyawan tsari don tabbatar da tsaron dukkan sojojin da aka tura a Mali kafin a mayar da su Jamhuriyar Nijar.