Mali na neman taimakon makobtanta | Duka rahotanni | DW | 01.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Duka rahotanni

Mali na neman taimakon makobtanta

Shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Keita, na ziyartan kasashe da ke iyaka da kasar don samun hanyar da za'a magance matsalolin tsaron kasar

Bisa wani mataki na neman kawo karshen rikicin da kasar ta Mali ke fama da shi, kungiyar mayakan sa kai ta Abzinawa Imrad da ke goyan bayan gwamnatin kasar, ta amince ta janye daga birnin Anefis wanda ta kwace daga hannun kungiyar 'yan awaren yankin Azawad na kasar a tsakiyar watan jiya. Tuni ma dai ta fara aikin tattare irin yanata-yanata daga birnin amma yanzu haka wasu daga cikin mayakan kungiyar na ci gaba da kasancewa a cikin garin na Anefis.

A kokarin da suke ne na neman maido da zaman lafiya a kasar ta Mali, masu shiga tsakani na kasa da kasa a cikin rikicin kasar a dai-dai lokacin da ake shirin cimma yarjejeniyar birnin Algers wacce za ta kawo karshen rikicin, suka bukaci ko wane daga cikin kungiyoyin mayakan kasar da ya janye daga cikin garuruwan da ya kama a baya-bayannan, domin komawa a matsayinsa na farko.

Kungiyar mayakan Abzinawan Imrad masu goyan bayan gwamnatin Malin, wadanda suka kwace birnin Anefis daga hannun mayakan kawancan kungiyoyin 'yan a waren Azawad bayan wani kazamin fada a tsakiyar watan jiya, na daga cikin wadanda kira ya shafa. Sai dai kungiyar ta GATIA ta ci gaba da yin kememe a kan matsayinta. Sai dai a cewar wakilin kungiyar ECOWAS a Mali Abdou Toure Sheka a halin yanzu kungiyar ta amince da ta janye a bisa manufa.

"Ya ce kungiyar ta fahimci cewa ba ta da wani zabi in ba na ficewa daga birnin Anefis ba, dan haka yanzu ga zancan da ake wata tawagar shugabannin kungiyar na kan hanyarta zuwa garin, domin tsara aikin janyewar. Tuni ma dai ta iso birnin Gao. Kuma muna sa ran nan da kwanaki biyu zuwa uku za su janye kwata-kwata."

Wannan bada hadin kai ga kiran janyewa daga birnin na Anefis da mayakan kungiyar ta GATIA suka yi, ya zo ne a daidai lokacin da Shugaban kasar ta Mali Ibrahim Boubacar Keita, ya soma wani rangadi a kasar Algeriya inda daga nan ya zarce zuwa kasar Nijar. David Vingerand wani masani siyasar kasar ta Mali ya ce wannan ziyara na da alaka da mataki da kungiyar ta GATIA ta dauka.

"Ya ce IBK ya je ne a kasar ta Algeriya domin ganawa da shugaban kasar, dama tattaunawa da shi a game da hanyoyin kawo karshen matsalar kasar ta Mali. Kuma batun janyewar mayakan kungiyar GATIA na daga ciki"

Saidai wata ayar tambaya a nan ita ce, su wa za su maye gurbin kungiyar ta GATIA daga wuraren da za ta janye. To amma wakilin kungiyar ta ECOWAS a kasar ta Mali, ya shaida wa gidan Radio DW rundunar zaman lafiyan ta kasa da kasa a kasar da ke aiki a Mali wato MUNISMA ce za ta maye gurbin kungiyar ta GATIA, domin ci-gaba da kula da tsaron lafiyar al'ummar birnin. Kuma kamar yanda yarjejeniyar birnin Algers ta tanada, za'a kafa wani kwamitin tsaro, wanda zai kumshi wasu man'yan sojojin kasar ta Mali dama wakillan kungiyoyin 'yan tawayen arewacin kasar . Wanda zai sa'ido da tabbatar da ganin ko wane bangare ya mutunta sharudan da yarjejeniyar birnin Algers din ta tanada

Sauti da bidiyo akan labarin