Makomar zaben ′yan gudun hijira a Najeriya | Siyasa | DW | 19.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Makomar zaben 'yan gudun hijira a Najeriya

Dokar da ta kafa INEC ba ta ce sai mutum yana da kati na din din din zai yi zabeba idan kana da tsoho ko sabon kati duk daya ne a cewar dan majalisa daga arewa maso gabas.

A yayinda zaben shekara ta 2015 ke kara karatowa a tarayyar Nigeryia, wata matsala da ake so a fuskanta itace ta kada kuri'ar dubban 'yan gudun hijra da rikici, ko ta'addancin 'yan Boko Haram ya tarwatsa su daga garuruwansu na iyaye da kakanni wanda kuma ake tababar ko zasu iya kada kuri'arsu a yayin zaben, kuma a ina zasu kada da wane irin katin zabe? Wannan ita ce babbar tambayar da ta shiga zukatan wadannann al'umma, musamman wadanda suka fice daga jihohin Borno Yobe da Adamawa amma a ra'ayin gwamnan jihar Borno Kashim Shettima tuni ya ware Naira miliyan goma dan a dauko awasu da ke gudun hijirar su dan su kada kuri'unsu kamar sauran 'yan kasa:

"Dole a mutunta Kampala Convention kuma baa kanmu aka fara ba akwai mutanen Okirika da aka kawo su su kayi zabe a Fatakwal, akwai mutanen Wusa a Taraba, akwai wadanda ke Maiduguri da Yola da Nijar har da Kamaru idan kuma sun ce mu ba 'yan kasa ba ne sai mu fice musu daga kasar"

Shi ma dai Ali Ndume dan majalisa daga yankin ya yi nasa tsokacin kamar haka:

"Dokar da ta kafa INEC ba ta ce sai mutum yana da kati na din din din zai yi zabeba idan kana da tsoho ko sabon kati duk daya ne"

Tshohon mataimakin shugaban majalisar tarayya Usman Bayero Nafada ya ce ya zama dole a ba wa mutane dama su yi wannan zabe tare da samar da tsaro ga dukkanin al'umma.

Sauti da bidiyo akan labarin