1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Makomar zabe da 'yan daba a Najeriya

Abdullahi Tanko Bala
March 28, 2019

A Najeriya kungiyoyin fara hula da masu rajin kare dimukurdiyya sun bayyana takaici a kan tabarbarewar yanayin zabe a Najeriya.

https://p.dw.com/p/3Fqmm
Nigeria Protest gegen Benzinpreise
Hoto: dapd

Kungiyoyin musamman sun nuna takaici yadda aka gudanar da zabe a wasu yankuna na jihohi biyar na Najeriya inda aka maimaita zaben gwamna da ba a kammala ba.

Kungiyoyin sun yi Allah wadai da amfani da ‘yan daba wadanda suka rika cin zarafin masu zabe tare firgita wanda suka ce hakan karan tsaye ne ga tafarkin dimukuraddiya a Najeriya.

Musamman matsalar tafi tazara a jihar Kano da wani sashe na jihohin Sokoto da Benue da kuma Bauchi. Matasa ne dai aka yi amafani da su a wannan abin takaici da aka kira da sunan zabe, a cewar Farfesa Jibo Ibrahim na cibiyar nazarin dimukurdiyya da ke Abuja.