Makomar tsaro a sabuwar gwamnatin Najeriya | Siyasa | DW | 03.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Makomar tsaro a sabuwar gwamnatin Najeriya

Samun nasarar Muhammadu Buhari a zaben shugaban Najeriya na 2015 ya samar da sabon fata a yaki da Boko Haram.

Mummunar barnar da matsalar rashin tsaro ta yi ga tarayyar Najeriya da ya sanya ta zama tsumagiyar kan hanya da ke shafar yara da manya ya sanya batun zama kan gaba a jerin bukatun da ‘yan Najeriyar ke fatan share masu hawayen da suka dade suna kwarara a fuskokinsu, musamman ma dai a yankin arewa maso gabashin Najeriyar.

Tun a jawabinsa na farko dai zababben shugaban Najeriyar Janar Muhammadu Buhari ya yi alkawari maida hankali sosai a wannan fanni na rashin tsaro da ya dade da zamewa Najeriyar dan hakin da ka raina da sanya gwamnatin mika kokon bara zuwa kasashen da a baya ake wa kalon suna bayan Najeriyar. Shin wane hasashe da ma tasiri ake kallon kasancewar zababben shugaban Najeriyar Janar Muhammadu Buhari zai yi a yaki da kungiyar Boko Haram a Najeriyar? Mallam Kabiru Adamu kwararre ne a harkar tsaro a kasar:

Boko Haram Kämpfer

Mayakan Boko Haram

"Kwarewar da ya ke da shi da kuma yarda da ake da ita a kansa, na farko yardar nan shi zai sa mutane goyo bayan hukuma, wanda a halin da ake ciki a yanzu a wannan gwamnatin babu. To ta wannan hanya za'a iya samun bayanai daga jama'a zuwa hukuma. Na biyu ka ga harakar cin hanci da rashawa to nasan za'a samu canji daga bangaren sojojin''.

A yayinda ake hasashen tasirin da zababben shugaban zai iya yi a yaki da aiyyukan ta'adanci ga Farfesa Rauf Mustapha manazarci a yaki da ta'adanci ya ce akwai matakan da ya kamata a yi la'akari da su:

‘'Baka da shi amma kaga wani ya rike abinda aka ce aba jama'a, talauci ma yakan kawo amma talauci na cutar mutane, kuma ya kamata a kare wa kowa hakinsa ya bi ta hanyar da yake so, amma fa ba wai sai ya takura wa jama'a ba''.

Nigeria Soldaten Offensive gegen Boko Haram

Dakaru da ke yaki da Boko Haram

Jan kafar da wasu kasashen duniya ke yi a kan taimaka wa Najeriya don shawo kan matsalar ya sanya karuwar matsalolin da ake fuskanta. Ko sauyin da aka samu na kasancewar Janar Buhari zai iya sanya su canza ra'ayinsu? Har ila yau ga Mallam Kabiru Adamu:

‘'Koken da suke yi a kan batun kare hakin jama'a ne wanda ake tunin sojojin Najeriya basa yi, muna sane da cewa akwai wurare da yawa, an danne hakin talaka, an ma kashe talakawa da yawa. A wasu wurare sai ka ji cewa yawan mutanen da sojoji suka kashe sun wuce wadanda su ‘yan ta'adan suka kashe, to duk koken bai wuce wannan ba, basa son ganin an yi amfani da taimakon da zasu bayar a kashe talakan da bai san hawa ba bai san sauka ba. To idan har gwamnatin shi Janar Buhari suka duba wannan suka ga yadda zasu gyara, to in har aka yi haka to kasashen da muke magana zasu bai wa Najeriya goyon bayan da ake magana''.

Al'ummar Najeriyar dai na masu zura idanu don ganin ci gaban da za'a samu a fanin samar da tsaro da ke zama kashin bayan duk wani ci gaba a cikin kasar.

Sauti da bidiyo akan labarin