Makomar Boko Haram bayan karbe Sambisa | Zamantakewa | DW | 29.12.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Makomar Boko Haram bayan karbe Sambisa

Makomar mayakan kungiyar Boko Haram na ci gaba da daukar hankali a Najeriya da kasashen da ke makwabtaka da ita kwanaki kalilan bayan da rundunar soji ta sanar da kame dajin Sambisa .

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sanar da cewar dakarun kasar sun karbe iko da babbar tungar 'yan Boko Haram da ke dajin Sambisa a jihar Borno, inda aka kame da dama a cikinsu. Tuni ma wasu mayakan Kungiyar Boko Haram suka mika wuya ga hukumomin Jihar Diffa ta Jamhuriyar Nijar.

DW.COM

Sauti da bidiyo akan labarin