Makarantu za su bude Satumba 22 a Najeriya | Siyasa | DW | 15.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Makarantu za su bude Satumba 22 a Najeriya

Duk da amincewa da bude makarantun da 'yan majalisun suka yi, sun ce ba za su lamunci sakaci wajen bin sharuddan da suka gindaya dan kare dalubai daga kamuwa da Ebola ba.

A Najeriya ministocin kula da harkokin ilimi da na lafiya sun gurfana a gaban kwamitin majalisar wakiklan Najeriya a game da takadamar da ake fuskanta a kan batun sake bude makarantun firame da sakandire saboda cutar Ebola.

‘Yan majalisar wakilan Najeriyar dai sun nuna damuwarsu ne a kan illar da ke tattare da bude makarantun na Najeriya a makon gobe a yanayin da ake ci gaba da fama da cutar ta Ebola, domin kaucewa abin da ka iya shafar lafiyar yaran kasa.

'Yan majalisa sun ce sun dauki matakan kariya.

Nationalversammlung in Abuja, Nigeria

'Yan majalisa sun ce gwamnati ta dauki matakan kariya nagartattu

Amma ministocin ilimin da na lafiya sun warware zare da abawa a kan matakan da tuni suka ce sun dauka don samar da kariya, domin an ci karfin cutar ta Ebola da har zuwa wannan lokaci a biranen Lagos da Fakwal ne kadai aka fuskanci matsalar don haka ba dalilin da zai sa a ci gaba da barin yaran a gida. DR Nasiru Sani Gwarzo shi ne ya wakilci minsitan kula da lafiya na Najeriya

Abin da yafi daukan hankali shi ne yadda kungiyar likitocin Najeriya wacce a baya ta bayyana adawarta a kan bude makarantun a yanzu ta sauya wannan matsayin nata abinda Dr Kayode Obembe shugaban kungiyar ya bayyana da cewa.

Duk da cewa ‘yan majalisun sun amince da a bude makarantun a ranar 22 ga watan nan, sun ce ba za su lamunci sakaci wajen bin sharuddan da aka gindaya a dauka ba, kamar yadda Hon Aminu Sulaiman shugaban kwamitin kula da harkokin ilimi na majalisar wakilan Najeriyar ya bayyana.

Sauti da bidiyo akan labarin