Makarantu a Gini sun buda kofofinsu | Labarai | DW | 13.02.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Makarantu a Gini sun buda kofofinsu

Mafi yawan 'yan makaranta a kasar Gini sun koma ga makatu, bayan da aka rufe makarantun kasar na tsawon lokaci sakamakon yaduwar cutar Ebola.

A kalla makarantu dubu 12 na kasar suka buda kofofinsu daga ranar 19 ga watan Janeru da ya gabata kawo yanzu a cewar asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF. An dai rufe makarantu sakamakon yaduwar cutar ta Ebola a kasashen Liberiya, Saliyo da kasar ta Gini da suka fi fama da wannan cuta. A ranar Litinin mai zuwa ce ake sa ran komawa ga makarantun na boko a kasar Liberiya, yayin da a watan Maris mai zuwa ake sa ran komawa ga makarantun a kasar Saliyo. Sai dai kuma labarun baya-bayannan na cewa an killace gidaje a kalla 700 har na tsawon kwani 21 a garin Aberdeen da ke kasar ta Saliyo, bayan rasuwar wani mai kamun kifi da aka gano cewa cutar ta Ebola ce ta kashe shi.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Suleyman Babayo