Majalisar Tarayyar Turai ta yi sabon shugaba | Labarai | DW | 18.01.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Majalisar Tarayyar Turai ta yi sabon shugaba

Majalisar Tarayyar Turai ta zabi Antonio Tajani dan asalin kasar Italiya, a matsayin sabon shugabanta.

Antonio Tajani, sabon shugaban majalisar Tarayyar Turai

Antonio Tajani, sabon shugaban majalisar Tarayyar Turai

Antonio Tajani dan asalin kasar Italiya ya samu nasarar zama sabon shugaban majalisar Tarayyar Turai. Tajani da ke zaman mai ra'ayin 'yan mazan jiya, ya samu nasarar ne bayan da aka gudanar da zagaye na hudu na zabe wanda aka gudanar a ranar Talatar da ta gabata a shalkwatar majalisar da ke birnin Strasbourg. Mai shekaru 63 a duniya ya gaji shugaban majalisar mai barin gado Martin Schulz wanda ke zama dan kasar Jamus. Tajani ya kasance mamba a majalisar ta Tarayyar Turai tun a shekara ta 1994.