1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar ministocin hadin kan kasa a Nijar

August 14, 2013

Shugaban jamhuriyar Nijar ya fito da sabuwar gwamnatin hadin kan kasar wacce aka jima ana cecekuce a kanta wadda ta kunshi wakilan jam'iyyun adawa.

https://p.dw.com/p/19Q5k
epa03142091 President of Niger, Mahamadou Issoufou delivers a speech during the opening ceremony of the 6th World water forum at Parc Chanot in Marseille, southern France, 12 March 2012. More than 1,000 high-level stakeholders are gathered in Marseille to share solutions to worldwide water problems and commit themselves to their implementation. EPA/GUILLAUME HORCAJUELO +++(c) dpa - Bildfunk+++
Hoto: picture-alliance/dpa

A jamhuriyar Nijar shugaban kasar ne ya fito da sabuwar majalisar ministocin hadin kan kasar wacce aka jima ana kai ruwa rana a kanta tun bayan da 'yan adawar kasar su ka yi watsi da tayin da shugaban ya yi masu na su zo a dama da su. Sai dai gwamnatin ta kunshi wasu kusoshin jam'iyyar MNSD NASARA madugar 'yan adawa duk da rashin amincewar uwar jam'iyyar tasu.

Sabuwar gwamnatin da shugaban Nijar din Alhaji Mouhamadou Issoufou ya kafa ta kunshi membobi 36 daga ciki mata biyar a karkashin jagorancin Fitaminista BIrji Rafini. Daga cikin ministocin biyar na da mukamin manyan ministoci na kasa wato Ministre d'etat daga ciki har da magatakardan jam'iyyar adawa ta MNSD NASARA Malam Albade Abuba da ya samu mukamin babban minista a fadar shugaban kasa.

Gebäude des Parlaments der Republik Niger, Niamey. Foto: Mahaman Kanta/DW, 19.5.2011, Niamey / Niger, Zulieferer: Thomas Mösch
Ginin majalisar dokokin Nijar a YamaiHoto: DW

Bakin fuskoki 21 ne suka shigo sabuwar gwamnatin daga ciki har da ma'aikacin gidan Rdiyon Deutsche Welle Malam Yahouza Sadissou Madobi na jam'iyyar RSD GASKIYA, biyar na jam'iyyar adawa ta MNSD NASARA da suka hada da Malam Alma Ummaru a mukamin ministan kasuwanci da kuma Salisu Ada shugaban matasan jam'iyyar ta MNSD NASARA da ya samu mukamin ministan samar da ayyukan yi da kuma Malam Wasalke Bukari da ya samu mukamin ministan ma'aikatar ruwa da tsabta. Ministocin tsohuwar gwamnati 10 zuwa 11 ne suka sake komawa a kan mukamansu daga ciki har da Malam Bazum Mohammed da Malam Moru Amadu da Ministan man fetur Fumakoy Gado.

Tsoffin ministoci biyarne suka dawo cikin gwamnatin amma da sabon mukami kamar su Malam Abdu Labo tsofon ministan cikin gida da ya samu mukamin ministan ma'aikatar noma ta kasa.

Titel: Seini Oumarou, Vorsitzender der Partei MNSD im Niger Schlagworte: Niger, Oumarou, Opposition, MNSD Wer hat das Bild gemacht?: offizielles Bild (MNSD) Wann wurde das Bild gemacht?: 2013 Wo wurde das Bild aufgenommen?: Niamey, Niger Bildbeschreibung: Bei welcher Gelegenheit / in welcher Situation wurde das Bild aufgenommen? Wer oder was ist auf dem Bild zu sehen? Seini Oumarou ist Vorsitzender der Partei MNSD-Nassara (Mouvement National de la Société de Développement ) und seit April 2011 Oppositionsführer im Niger. Zuvor hatte er in der Stichwahl um die Präsidentschaft gegen Mahamadou Issoufou verloren.
Seini Oumarou shugaban MNSDHoto: MNSD

Da yake tsokaci jim kadan bayan bayyana jerin sunayen sabbin membobin gwamnatin babban magatakardan gwamnati Malam Gandu Zakara ya bayyan cewa: "Wannan gwamnati ce fadadda da ta kunshi dukkanin bangarorin siyasa na Nijar da kuma ya hada maza da mata kwararru daga bangarori daban-daban na al'umma. Wasu za su iya kiran ta gwamnatin hadin kan kasa wasu kuma su kira ta na kowa da kowa, to koma me za a kira ta dai wannan gwamnati ce dake da gurin damawa da duk 'yan Nijar da suke shirye su yi wa wanann kasa aiki."

Tuni dai al'ummar kasar suka soma tofa albarkacin bakinsu kan wanann sabuwar gwamnati.

Abun jira a gani dai a nan shi ne yadda jam'iyyar MNSD NASARA za ta karbi nada wasu 'ya'yan nata da ma kuma tasirin da sabuwar gwamnatin za ta yi wajen warware matsalolin da suka dabaibaye tafiyar kasar ta Nijar a yanzu.

Mawallafi: Gazali Abdu Tasawa
Edita: Mohammad Nasiru Awal