Majagin garin London ya goyi bayan ficewar kasar daga EU | Labarai | DW | 22.02.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Majagin garin London ya goyi bayan ficewar kasar daga EU

A ranar Lahadin nan ce magajin garin birnin London Boris Johnson ya bayyana cewar a shirye yake wajen ganin ya goyi bayan ficewar Britaniya daga cikin kungiyar EU.

Matakin na magajin garin London din ya zone a matsayin wani babban koma baya ga Firiminista David Cameron wanda kwana daya tak kafin magajin garin ya furta kalaman bayan da Firiministan ya ce za a gudanar da kuri'ar raba gardama a ranar 23 ga watan Yuni da ke tafe.

Boris Johson ya kara da cewar,

"Na yanke hukuncin ne bayan nisan tunani da kaiwa da komowa, kuma abu na karshe da zan iya yi shi ne na saba da muradin David Cameron ko kuma gwamnatin, ina goyan bayan ficewa daga kungiyar ko da kuwa me za a ce."