Libiya: Mai ya jawo hadarin jirgin al-Haddad?
December 25, 2025
An dai ayyana zaman makoki na kwanaki uku a kasar Libiya, kan abun da aka kira da babbar asarar da kasar ta yi wacca zai yi wuya a iya maye gurbinta. Tuni tawagar binciken kwakwaf ta kasar ta Libiya ta isa birnin Ankara na kasar Turkiya, domin gudanar da nata binciken kan hakikanin musabbabin mutuwar marigayi Laftanar Janar Mohammad al-Haddad da masu dafamar baya su shida.
Ma'aikatar cikin gidan Turkiyya dai, ta sanar da gano burakuzan jirgin da gawarwakin mamatan gami da bakin akwatin jirgin saman da ya yi hadari da janar din, kamar yadda ministan ma'aikatar cikin gidan Turkiyya Ali Yerlikaya ya nuna hotunan da tauraron dan Adam ya dauka na hadarin jirgin.
Zaman makoki da jimami
Firaministan Libiya Abdul Hamid Dbeibeh ya sanar da rasuwar babban hafsan sojin kasar da wasu manyan jami'an sojin kasar, sakamakon mummunan hadarin, yayin da suke komawa gida daga wata ziyarar aiki a Turkiyya kamar yadda ya wallafa bakin cikinsa a shafinsa na X.
Firaministan ya ce hadarin ya faru ne a lokacin dawowarsu daga babban birnin Turkiyya Ankara, ba tare da ya bayar da karin bayani kan abin da ya haifar da shi ba. Ya bayyana cewa wannan babban rashi ne ga kasa da rundunonin soja, kuma ya ce Libiya ta rasa maza da suka yi wa kasarsu hidima da “gaskiya da ladabi da kwazo, tare da mika ta'aziyya ga iyalai da abokan aikinsu da ma al'ummar kasar.
An rasa hanyoyin sadarwa da jirgin tun kusan karfe takwas da mintuna 52 na yamma agogon Turkiyya, a yayin da jirgin ke hanyarsa ta komawa Tripoli. Jirgin ya aike da sakon gaggawa na neman dawowa da sake sauka kusa da Haymana, kuma tun daga nan ba a sake jin duriyarsa ba.
Ma'aikatar tsaron Turkiyya ta sanar a baya cewa babban hafsan sojin na Libiya na ziyara a Ankara, inda ya gana da takwaransa na Turkiyya da wasu manyan kwamandojin soja, ziyarar na cikin matakin hadin gwiwar soja da ta tsaro da ke gudana tsakanin kasashen biyu.
Ina makomar shirin hada kan kasa?
Tuni dai babban abokin hamayyar marigayin Janar Khalifa Haftar da ke zama babban hafsan sojin gabashin Libiyan, ya mika sakon ta'aziyarsa na rashin mutumin da ya siffanta da gwarzo mai kishin kasa. A na dai fargabar cewa, mutuwar al-Haddad din za ta bar gagarimin gibin tsaro a gwamnatin ta Debaibah da ke fama da matsalolin tawayen kananan hafsoshin soja, wadanda al-Haddad ya yi nasarar kawar da su ko dakushe su.
Kamar yadda ake fargabar cewa, shirin da ya gabatar na ganawar manyan hafsoshin sojan Libiya 10, biyar daga gabashin kasar da kuma wasu biyar daga yamamcinta domin dunkulewar kasar zai iya bin ruwa, kasancewar shi ne wanda yafi zakewa don ganin shirin ya yi nasara.