Asarar rayuka a yake-yaken kasar Libiya | Labarai | DW | 21.05.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Asarar rayuka a yake-yaken kasar Libiya

An kashe sojoji da dama a wani sabon fada a kasar Libiya yayin da wasu kuma da dama suka samu raunuka a wannan kasa da ke fama da yakin basasa.

Akalla sojoji goma sun rasu tun a ranar Laraba a wani dauki ba dadi da aka yi a birnin Bengazi, yayin da wasu 36 suka samu raunuka. Sannan kuma an kashe wani mayakin kungiyar Fajr Libiya a kusa da birnin Misrata a wani harin da kungiyar IS reshen kasar ta Libiya ta dauki alhakin kaishi.

Birnin na Bengazi da ke a matsayin cibiyar tada kayar baya a kasar ta Libiya, na fuskantar matsalar yake-yake tun bayan rushewar gwamnatin marigayi Moammar Kadhafi a shekarar 2011. A tsawon shekara guda fadan na Bengazi ya haddasa rasuwar mutane fiye da 1700 tare da ficewar wasu miliyoyin mutanen don tsira da rayukansu.